1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Amurka da Iran sun kai wa juna sabbin hare-hare

March 7, 2026

Amurka da kuma Isra'ila sun yi luguden wuta kan Tehran, ita ma Iran ta kai hari Tel Aviv.

Amurka da Iran sun kai wa juna sabbin hare-hare a rana ta takwas
Amurka da Iran sun kai wa juna sabbin hare-hare a rana ta takwasHoto: Fatemeh Bahrami/Anadolu Agency/IMAGO

Rundunar tsaron juyin juya halin Iran (IRGC) ta bayyana a ranar Asabar cewa ta kai hari kan sansanin sojin Amurka na Juffair da ke Bahrain.

Ta ce an yi amfani da sansanin wajen kai hari kan tashar tsarkake ruwan teku ta Qeshm a Iran tun da farko.

Iran ta nemi afuwar kasashe makwafta kan hare-harenta

A cikin wata sanarwa da rundunar ta wallafa a shafinta na intanet, ta ce harin wani ɓangare ne na matakan da take ɗauka na mayar da martani ga hare-haren  Amurka.

A nata bangaren isra'ila da Amurka sun kaddamar da luguden wuta a birnin Theran inda suka far wa filin jirgin kasar da rumbunan mai da kuma muhimman wuraren gwamnati.

Na rufe kofar tattaunawa da Iran - Trump

Dubban mutane sun taru domin yin zanga-zanga a biranen Berlin da Düsseldorf a ƙasar Jamus, suna neman a samar wa Iran 'yanci ta hanyar dakatar da yaki, kamar yadda ‘yan sanda suka bayyana a ranar Asabar.

Zanga-zangar ta zo ne kusan mako guda bayan hare-haren da Israel da Amurka suka kai kan Iran.

Wani kakakin ‘yan sanda ya ce kimanin mutane 1,000 ne suka taru kusa da kofar Brandenburg a Berlin, duk da cewa mutane 2,000 ne suka yi rajistar halartar zanga-zangar. 

Ya ƙara da cewa taron ya gudana cikin lumana ba tare da wata matsala ba har zuwa yammacin yau Asabar.

Masu jawabi a wurin taron sun tuna da dubban mutane da aka kashe a zanga-zangar da aka yi a farkon shekarar nan a Iran.