1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Amurka da Iran za su ci gaba da tattauna kan nukiliya a Rome

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
May 23, 2025

A ganawar karshe ta wakilan an tashi baram-baram sakamakon yadda Iran ta ce babu mai hana ta habaka makamashin uranium.

Shugaban Amurka Donald Trump da jagoran addinin Iran Ali Khamenei

A Juma'ar nan za a ci gaba da zaman tattaunawar sulhu tsakanin wakilan Amurka da na Iran a birnin Rome na kasar Italiya, game da yarjejeniyar dakatar da kera makamashin nukiliyar Iran, wadda ta dage cewa babu mai iya hana ta ci gaba da bunkasa sarrafa ma'adanin uranium wanda ya kai matakin kashi 60 cikin 100 yanzu.

Karin bayani:Iran ba za ta daina bunkasa uranium dinta ba

A ganawar karshe da wakilan kasashen biyu suka gudanar a birnin Musqat na kasar Oman an tashi baram-baram, bayan gaza cimma matsaya sakamakon yadda Iran ta kekasa kasa ta ce ba gudu ba ja da bayan kan abin da ta sanya a gaba na habaka uranium.

A cikin watan Afirilun da ya gabata bangarorin biyu suka fara tattaunawa bayan sake dawowar Donald Trump a matsayin shugaban Amurka zango na biyu, wanda dama can shi ne ya fitar da Amurka daga yarjejeniyar a shekrar 2018 lokacin zangon mulkinsa na farko.

Karin bayani:Iran da Amurka sun gaza sasantawa a Oman

Daga cikin mahalarta taron ganawar keke-da-keken da ake kyautata zaton gani akwai ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi da kuma wakilin Amurka na musamman a Gabas ta Tsakiya Steve Witkoff.