1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amurka da Rasha na gasa tsakaninsu don yin tasiri a Sahel

Nikolas Fischer Saad Said Abubakar/Mouhamadou Awal
February 5, 2026

Amurka na sauya tsarinta da kamun ludayinta don samun karbuwa a kasashen Mali, Nijar da Burkina Faso, yayin da Rasha ke fadada tasirin rundunar sojojin hayarta ta Africa Corps a yankin Sahel.

Mali, Burkina Faso da Nijar sun kulla dangantaka da Rasha tun lokacin da sojoji suka karbi mulki a jerin juyin mulki
Mali, Burkina Faso da Nijar sun kulla dangantaka da Rasha tun lokacin da sojoji suka karbi mulki a jerin juyin mulkiHoto: Florent Vergnes/AFP/Getty Images

Ministan harkokin wajen Mali Abdoulaye Diop, ya karbi bakuncin wani babban jami'in Amurka domin tsara "sabon zubi" na dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu. Nick Checker, wanda ke jagorantar harkokin Afirka a ma'aikatar harkokin wajen Amurka, ya yi amfani da wannan dama wajen girmama 'yancin cin gashin kan Mali.

Dama kafin ziyararsa, Checker ya wallafa a shafinsa na X cewa Amurka na son "tattaunawa da sauran gwamnatoci a yankin Sahel ciki har da Burkina Faso da Nijar kan harkokin tsaro da tattalin arziki da aka raba."

Amurka na magance kura-kuran da ta tafka a baya 

Ziyarar Checker a Mali ta zo ne lokacin da Rasha ke ƙara yin tasiri a yankin SahelHoto: U.S. Department of State/Bureau of African Affairs/X

"A bayyane yake cewa Amurkawa ba su damu da dimukuradiyya a yankin Sahel a yanzu ba," in ji Ulf Laessing, darektan gidauniyar Konrad Adenauer a yankin sahel, inda ya ce: "Sun dauki matakin da ya dace da zamani. Wannan na nufin cewar jami'an Amurka na son gyara "kuskuren manufofinsu na baya."

Mali, Nijar da Burkina Faso sun katse ko kuma sun rage dangantaka da Faransa da ta yi musu mulkin mallaka da sauran abokan hulda na yammancin duniya, inda suka rungumi kasar Rasha. Sannan sun raba gari da makwabtansu na kasashen kungiyar ECOWAS ta yammacin Afirka  tare da kafa kungiyarsu ta yankin Sahel (AES).

"Ya kamata mu yi maraba da damar da Amurka ta bai wa kasashen AES da Faransa da EU ke son mayarwa saniyar ware, don tattaunawa," in ji Dr. Gnaka Lagoke, malami a fannin tarihi a Jami'ar Lincoln da ke Pennsylvania.

Taimakon Rasha wajen dakile hare-hare a Nijar da Mali

Mali ta fada cikin matsalar tsaro tsaro tun daga shekarar 2012, inda sojojinta ke fafatawa da kungiyoyin 'yan ta'adda ISWAP da na JNIM mai alaka da Al-Qaeda. Gwamnati ta yi alkawarin dakile ta'addanci, amma hare-haren na ci gaba da wakana. Sannan a baya bayan nan, an kai hari a filin jirgin sama na birnin Nijar, Niamey, wanda ISWAP ta dauki alhakinsa.

Shugaban mulkin sojin Burkina Faso Ibrahim Traore yayin ziyara ga Putin a MoscowHoto: ZDF/DW

Amma ziyarar Checker ta zo ne a daidai lokacin da Rasha ke fadada tasirinta a yankin Sahel, ciki har da aika sojoji na haya na rundunar Africa Corps.

"Rundunar sojojin Afirca Corps ta ma'aikatar tsaron Rasha da Sojojin Nijar sun hada gwiwa wajen dakile harin, inda suka kashe 'yan ta'adda kusan 20 tare da kwace makamansu" in ji ma'aikatar harkokin wajen Rasha a cikin wata sanarwa.

Rundunar ta Rasha "za ta ci gaba da bayar da gudummawa mai kyau wajen karfafa tsaron yankin, tare da taimakawa da nufin kara karfin shirin yaki na sojoji ta hanyar horar da jami'an tsaro," in ji sanarwar.

Kungiyar JNIM ta kai wani hari kwanan nan a Mali, inda majiyoyi suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa akalla direbobi 15 ne suka mutu a wani hari da aka kai kan ayarin tankokin mai.