Amurka da Rasha na tattaunawa kan yakin Ukraine
February 18, 2025![Sergei Lavron na Rasha da Marco Rubio na Amurka na tattaunawa kai tsaye kan yakin Ukraine a Riyadh](https://static.dw.com/image/71658787_800.webp)
Sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio da takwaransa na Rasha Sergei Lavrov sun fara tattaunawa da ke zama ta farko ta keke da keke da manyan jami'an kasashen biyu. Dama sassan biyu na zaman doya da manja sakamakon kaddamar da farmakin da Rasha ta yi kan Ukraine da mamaye wasu daga cikin sassanta da nufin kawar da halin zaman tankiyar da ke tsakaninsu . Sannan suna neman share fagen zaman cimma yarjejeniyar kawo karshen yaki tsakanin Ukraine da Rasha da ake sa ran za ay yi nan gaba tsakanin shugabanin kasashen Amurka da Rasha da Ukraine a birnin na Riyadh.
Karin bayani:Yakin Ukraine na kara yin muni
Ba a gayyaci ita kanta Ukraine da ake takun saka tsakanin kasashen biyu a kanta ba. Sannan kasashen Turai da suka fi cutuwa da yakin na Rasha da Ukraine ba su samu goron gayyatar taron na birnin Riyadh ba, ko da yake,kamar yadda sakataren harkokin wajen Amurka,Rubio ke cewa, kasarsa na son bin batun da ke da matukar sarkakiya daki-daki ne:
Rubio ya ce: " Wannnan ba karamin aiki ba ne da ka iya kawo karshen yakin shekaru uku cikin zaman 'yan kwanaki, a daidai lokacin da kowane bangare ke kufule. Wannan taro ne na lalubo hanyoyin warware matsala ba na sake dagulata ba. Mune neman cimma maslaha tsakanin dukkaknin bangarorin. Mun yi ammanar cewa, ko da Ukraine ba a gayyace ta a wannan zaman tattaunawar ba, manufar dadada mata, ita ce kawo karshen yaki."
Karin bayani: Ukraine: Rasha ta cika kwanaki 1000 da mamaya
Tuni shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky, wanda yanzu haka yake ziyara a Hadaddiyar Daular Larabawa, yana shirin isa birnin na Riyadh a ranar Larabawa don ganawa da mahukuntan kasar ta Saudiyya kan wasu batutuwan na daban, inda ya caccaki tattaunawar ta jami'an Amurka da Rasha, yana mai shan alwashin cewa, ba zai yiwu a ci wa kasarsa albasa da baki ba:
Zelensky ya ce: " Kamata ya yi tsarin irin wannan taron tattaunawa kan wannan yakin ya kasance Amurka ta faro shi ne da tattaunawa da Turai, kana ta tattauna da mu kafin ta ce za ta tuntubi Rasha ko ma tattaunawa da ita kan makomar kasarmu da makomar nahiyar Turai ba. ba za mu lamunta da shi ba. "
Sai dai a nasa bangaren, ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov, ya ce in don ta kasashen Turai za a biye wa, har abada ba za a shirya wannan taron ba. Ya ce: " Ban ga amfanin gayyatar su zuwa wannan taron na Riyadh ba, saboda dagewar da suke yi wajen lalata duk wani yunkurin sasantawa. Ban san irin dabi'u da al'adun da suke bi da ke koya musu irin wannan mummunan tunanin na ci-gaba da jan kafa wajen sasantawa a madadin warware illahirin wannan matsalar ba."
Karin bayani:Ya Koriya ta Arewa za ta sauya yakin Ukraine?
Tun bayan da shugaban Amurka Trump ya buga waya ga shugaban Rasha Putin, kana suka cimma matsaya kan wajibcin kawo karshen yakin Rasha da Ukraine, kasashen Turai suka fusata da yadda ake kokarin mayar da su saniyar ware dangane da yakin da yayi sanadin jefas u cikin matsalolin tattalin arziki kuma barazana ga tsaronsu. Shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya karɓi bakuncin taron manyan ƙasashen Turai don tattaunawa kan batutuwa masu alaka da tsaron yankin da kuma barazanar da suke fuskanta daga Donald Trump na Amurka, musamman matakan da yake dauka na kawo karshen yakin Ukraine.