1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

300810 USA Terrorismus

August 30, 2010

CIA ta bayyana cewar 'yan tarzoman Yemen sun fi hatsari akan Al-Kaida dake Pakistan.

Headkwatar CIAHoto: Wikipedia/Pd THOR

Ga hukumar leken asiri ta CIA ta Amurka dai reshen 'yan Al-Kaida na Yemen na kasancewa wata babbar barazana. A karon farko bayan harin 11 ga watan Satumba, hukumar ta bayyana cewar 'yan tarzoman na Yemen sun fi hatsari akan cibiyar Al-Kaida dake Pakistan. A yanzu haka dai gwamnatin Amurkan na la'akari da tura CIA ɗin zuwa Yemen. Akwai Bidiyoyi dai dake nuna yadda mayakan Al-Kaida ke ihu a sansanonin horar da su, irin hotunan dake razana 'yan siyasar Amurka.

Ana iya jin mai tsattsauran ra'ayin nan Imam Anwar Al-Awlaki na bukatar kira da a yaƙi Amurka.

Sojojin Amurkan dai sun dauki shekaru masu yawa suna aiki tare da sashin yaƙi da ayyukan tarzoma na ƙasar Yemen , duk kuwa da cewar a asirce suke tafiyar da ayyukan haɗin gwiwar. A karkashin gwamnatin Barack Obama kuwa, a bara ne aka daɗa ƙarfafa wannan dangantaka na aiki kafaɗa da kafaɗa tsakanin ɓangarorin biyu.

Anwar al-AwlakiHoto: dapd

An gano cewar sojan da ya buɗe wuta a sansanin sojojin Fort Hood na Amurka har ya kashe mutane 13, yana da alaka da Limami Al-Awlaki. Kana matashi Ɗan Nigeriyar nan da yayi yunƙurin tarwatsa wasu sinadrai a cikin jirgin Amurka a ranar Krisimetin shekarar data gabata ya kasance a ƙasar ta Yemen.

Tun bayan nan ne aka rika gabatar da rahotanni dangane da harkokin tarzoma na ƙungiyar Al-kaida a yankunnan da ake tsirarun kabilu, da kuma irin raunin da gwamnati ta ke dashi.

Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton ta yi gargaɗin cewar rashin zaman lafiya a Yemen barazana ce wa yankin da ma Duniya baki ɗaya a fannin tsaro.

Yanzu daya fito fili cewar hukumar CIA ta Amurka ta bayyana Al-kaidan na Yemen da kasancewar mafi hatsari fiye dana Pakistan,ya bawa mutane da dama mamaki. A yanzu hakan dai ƙungiyar tana gaza cimma burinta na kai hare-hare fiye da samun nasara. Domin bayan yunƙurin harin na ranar Krisimeti akan jirgin Amurka, kaza lika a watan Mayu an gano wasu boma bomai da aka dasa a dandalin New York Times, kafin ya tarwatse.

Hoto: picture alliance/dpa

To sai dai ƙwararru kan harkokin tsaro a Amurkan sun bayyana ta hanyoyi aikewa da sakonni a rubuce cewar yana da muhimmanci acigaba da mayar da hankali kan Al-kaida dake ƙasar Pakistan.

Amma hukumar ta CIA na ganin cewar Al-kaida da ke Yemen sun fi ƙarfi da tsauri, don haka suka mayar da hankalinsu kacokan kan Imam Alwar Al-Awlaki.

Imam Al-Awlaki dai haifaffen Amurka ne, wanda yake yara harshen Turanci sosai, kamar yadda CIA tayi nuni dashi. Sakamakon wannan sabon nazari da hukumar leken asirin Amurkan ta CIA ta yi dai, a yanzu haka Washinton na la'akari da tura jami'an tsaro domin taimakawa harkokin tsaro.

Adangane da wannan hali da ake ciki ne dai Amurkan ta fara shirin yaƙi da ayyukan tarzoma a Pakistan, za kuma su mayar da hankali ba wai kawai kan manyan shugabannin Taliban da El-kaida ba, amma har da masu kai harin rokoki da haddadasa asarar rayukan fararen hula.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar

Edita : Umaru Aliyu