Amurka na daf da dawo da sayar wa Saudiyya da makamai
May 26, 2024![Antony Blinken da Mohammad Bin Salman na Saudiyya](https://static.dw.com/image/67102372_800.webp)
Akwai yiwuwar Amurka za ta iya janye matakin haramcin sayar wa Saudiyya da manyan makaman yaki cikin 'yan makonnin da ke tafe, kamar yadda jaridar Financial Times ta ruwaito a yau Lahadi.
A cewar jaridar Amurkar ta riga da ta sanar wa da Saudiyya batun janye dokar haramcin, a cewar wata majiya mai tushe mai cikakkiyar masaniya kan lamarin.
Jim kadan bayan kama aiki ne dai a shekara ta 2021, Shugaba Joe Biden ya tsaurara matakai kan musamman hare-haren Saudiyya a kan mayakan Houthi a Yemen, abin da ya haddasa mace-macen fararen hula.
Akwai ma batun zargin da Saudiyyar ke fuskanta kan take hakkin dan Adam, musamman na kisan dan jaridar nan Jamal Khashoggi a shekara ta 2018.
Saudiyya dai babbar abokiyar cinikin makamai ce a duniya musamman ma ga kasar Amurka.