1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaArewacin Amurka

Amurka na son a kawo karshen yakin Ukraine a Yuni

Mouhamadou Awal Balarabe
February 7, 2026

Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya bayyana cewa Amurka ta gayyaci wakilan kasarsa da Rasha don ci gaba da tattaunawa a mako mai zuwa a brinin Miami, domin ganin an kawo karshen yaki kan nan da watan Yuni mai zuwa.

Zelensky da Trump a taron manema labarai a Mar-a-Lago da ke Amurka
Zelensky da Trump a taron manema labarai a Mar-a-Lago da ke AmurkaHoto: Jim Watson/AFP

A yayin wani taron manema labarai da ya gudanar, Zelensky ya amince da goron gayyatar Amurka, amma ya sake nanata cewa kasarsa ba za ta amince da duk wata yarjejeniya da aka cimma tsakanin Amurka da Rasha ba tare da sahalewar Kyiv ba, musamman kan batutuwan da suka shafi yankunan da ake takaddama a kai.

Karin bayani: Shawari 28 na sasanta Ukraine da Rasha

Rasha, wacce ta kaddamar da farmakin soji kan Ukraine a 2022, ta mamaye kusan kashi 20% na kasar kuma tana kokarin samun cikakken iko a yankin Donetsk da ke gabashin Ukraine, tana barazanar kwace shi da karfi idan tattaunawar ta gaza cimma biyan bukata.

Sannan Moscow na neman Ukraine ta janye sojojin Ukraine daga wasu sassan yankin da har yanzu suke iko da shi, bukatar da Ukraine ta ce ba za ta amince da ita ba.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW