Amurka ta ayyana hana Visa ga wasu 'yan Najeriya
December 4, 2025
A baya dai kasar ta Amurka ta yi barazanar kaddamar da jerin hare hare harie hare a cikin tarayyar Najeriyar da nufin kare kiristocin da ta ce suna fuskantar barazanar kare dangi.
Kuma wani kamfen da ya dauki hankali har a cikin majalisar wakilan Amurka ya nemi a sanya tarayyar Najeriyar cikin jeri na kasashen da ke a kan gaba cikin danyen aikin.
Kafin sabon matsayin mahukuntan na Washington da ke nuna alamun sauyin rawa bisa makoma ta kiristan.
Karin Bayani:Amurka za ta hana masu kisan Kiristocin Najeriya biza
A karkashin sabon matsayin dai duk wanda ya bada umarni, ko jagoranta, da ma goyon bayan batun na kisan kiristoci zai fuskanci takunukumin hana shi damar shiga kasar ta Amurka.
Sabon matsayin na Amurka dai ya biyo bayan kai kawon makonni na jami'an Najgeria zuwa Washington, da ma jerin matakan wankin suna cikin tarayyar Najeriyar.
Kuma daga dukkan alamu matakin na Amurka na shirin burge kiristocin da ke ikirarin ji a jiki, a tunanin Reverand Joseph Hayab da ke zaman shugaban kungiyar kiristocin kasar reshen arewacin tarayyar Najeriyar.
Karin Bayani:Tinubu ya mayar da martani kan barazanar Trump
Karin Bayani:Ina makomar dangantakar Amurka da Najeriya?
Kokarin kare ta‘adda, ko kuma kara jefa daukacin kasar cikin halin rudu, a cikin tsakiyar nunin yatsa bisa batun gallaza wa kiristoci na zaman makiyayan da mafi yawansu ke zaman kabilar Fulani kuma a tunanin Usman Baba shugaban kungiyar makiyaya ta Miyyeti Allah, sabon matsayin na Amurka na iya kara jawo rabuwa cikin kasar da ke da addinai da kabilu daban daban.
Jan aikin da ke gaban Washinton da kila ma abokan takun da ke Abuja dai na zaman iya tantance masu goyon bayan tadda da kila ma tasirin hana damar shiga kasar Amurka a bangaren barayin dajin da babban birninsu ke a dazukan kasar