Amurka ta bude sabon babin takaddama da kotun ICC
August 20, 2025
Faransa ta nuna rashin jin dadi kan matakin kakaba wa wasu alkalan kotun kasa da kasa dake hukunta manyan laifuka ta ICC takunkumi da Amurka ta sanar.
Kotun ICC ta ce ana ci gaba da tafka laifukan yaki a yankin Darfur
Ma'aikatar harkokin wajen Faransar ta ce ta damu matuka da jin matakin na Amurka kan alkalan guda hudu, wanda ta ce matakin ya yi hannun riga da manufofi na daidaito da adalcin kotun.
A nata bangare ita ma dai kotun ta ICC ta fitar da wata sanarwa, tana mai cewar takunkumin na Amurka kan alkalanta ba komai ba ne face wani hari ne kai tsaye a gareta.
Kotun ICC ta bada sammacin cafke jagoran gwamnatin Taliban
A wannan Labarar ce dai babban sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio, ya sanar da matakin Amurkar na lafta takunkumi kan alkalan kotun hudu, bisa hujjar rawar da suka taka na ba wa kotun zarafin yin bincike da kama Amurkawa ko Isra'ilawa ba tare da hurumin kasashen biyu ba.