1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Amurka ta dakatar da kai sabbin hare-hare Iran

August 2, 2026

Shugaba Donald Trump, ya jingine batun kai sabbin hare-hare kan Iran, domin bude kofar cimma yarjejeniyar diflomasiyya.

Sojojin Amurka a fagen daga
Sojojin Amurka a fagen dagaHoto: Armin Weigel/AFP

A cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Truth Social, Trump ya ce dakatar da hare-haren na da sharadin cewa za a cimma yarjejeniya cikin gaggawa.

Karin bayani: Amurka da Iran na ci gaba da musayar wuta bayan janye sulhu

Ya bayyana cewa sojojin Amurka na cikin cikakken shiri domin kai hare-hare idan bukatar hakan ta taso, amma ya ce Iran da wasu ƙasashen yankin sun buƙaci Washington ta dakatar da farmakin saboda an riga an cimma "ginshiƙan yarjejeniya."

Karin bayani: Iran: kawayen Amurka za su fuskanci hare-haren ramuwar gayya

A gefe guda, ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya yi gargaɗin cewa Tehran za ta mayar da mummunan martani idan Amurka ta sake kai mata wani hari.

Rahotanni sun kuma bayyana cewa Yarima mai jiran gado na Saudiyya, Mohammed bin Salman, ya tattauna da Trump tare da nuna damuwa kan yiwuwar sabbin hare-hare daga Iran wanda ka iya dagula al'amura a yankin, inda ya buƙaci warware takaddamar da ke tsakani ta hanyar diflomasiyya.