SiyasaGabas ta Tsakiya
Amurka ta fara killace mashigin Hormuz
April 14, 2026
Talla
Rundunar sojin ta ce za ta fara killace dukkanin tashoshin jiragen ruwa da yankunan gabar tekun Iran, abin da ya fusata alkwarin da shugaban Amurka Donald Trump ya yi a baya na toshe mashigar Hormuz din da ke da muhimmanci ga kasashen duniya. Trump yace
"Ba za mu taba barin wata kasa ta yi wa duniya bakin ciki ba ko ta jefa duniya cikin masifa ba, Amurka ba ta bukatar wannan mashigin muna manmu wanda ya fi yawan na Saudiyya har da Rasha, kuma zuwa badi za mu rubanya adadin man da muke fitarwa, don haka ba mu bukatar mashigin amma duniya na matukar bukata. "