Trump ya gabatar da sabon shiri na dakatar da yakin Gaza
September 25, 2025
A daidai lokacin da sojojin Isra'ila ke kara zafafa hare-hare da suka yi ajalin mutane da dama a yankin Falasdinu, manzon Amurka Steve Witkoff ya ce Shugaba Trump ya gabatar da wani sabon shiri mai kunshe da tanade-tanade guda 21 na samar da zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya a yayin ganawarsa da kungiyar kasashen Larabawa da na Musulmi, daura da taron koli na MDD a birnin New York.
Karin bayani: Gaza: Shawarar Trump za ta kawo karshen yaki?
A cewar Steve Witkoff wannan shiri da Trump ya gabatar wanda kuma ba a fayyace shi ba, ya yi daidai da muradun Isra'ila da na kasashen yankin wadanda suka tabbatar da cewa za su ba da hadin kai.
A daidai wannan lokaci hukumar kare fararen hula ta Gaza ta ba da rahoton mutuwar mutane akalla 40 a ranar Laraba, 22 daga ciki sun gamu da ajalinsu ne a yayin hari ta sama da sojojin Isra'ila suka kai a wata mafakar 'yan gudun hijira a kusa da kasuwar Firas.