Amurka ta gabatar da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza
May 30, 2025
Wani daftarin yarjejeniya da Amurka ta gabatar ya nuna bukatar tsagaita wuta har na tsawon kwanaki 60 a zirin Gaza kamar yadda kafar yada labarai ta Reuters ta ruwaito.
Daftarin ya kuma bukaci a saki rayayyu da kuma matattun Isra'ilawa 28 da ke hannun Hamas a makon farko na fara aiki da sabuwar yarjejeniyar ta Washington.
Haka kuma ta nuna bukatar sako fursunoni Falasdinawa 125 da aka yanke wa hukuncin daurin rai da rai da kuma wasu 180 da suka riga suka mutu.
MDD ta kadu kan yawan mutane da ke bukatar agaji a Gaza
Yarjejeniyar da aka nuna ta na dauke da goyon bayan shugaban Amurka Donald Trump da kasashen Qatar da Masar ta kuma nuna bukatar shigar da kayan agaji Gaza da zarar Hamas ta amince da ita.
Har ila yau, ta kuma ce Hamas za ta saki sauran mutanen Isra'ila da ke hannunta su 30 a musayar karshe da bangarorin biyu za su yi idan har aka cimma tsagaita wuta na din-din-din.
Isra'ila za ta fadada matsugunan Yahudawa
Rahotanni dai sun bayyana cewa Hamas ba ta kai ga amincewa da yarjejeniyar ba saboda acewarta tamkar amincewa ne da ci gaba da kashe mutane.
A wani batun kuma shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce akwai bukatar kasashen Turai su tsaurara matsayarsu a kan Isra'ila idan har ba ta yi abinda ya dace ba dangane da shigar da kayan agaji zirin Gaza.
Kalaman na Macron na zuwa ne a dai-dai lokacin da Isra'ila ke kara fuskantar matsin lamba daga duniya kan halin yunwa da Falasdinawa ke ciki a Gaza.
Mista Macron din ya kara da cewa akwai bukatar daukar mataki a cikin sa'o'i masu zuwa ko kuma kwanaki na nan gaba domin taka wa Isra'ila birki.
Har ila yau, ya kuma nuna bukatar amincewa da Falasdinu a matsayin kasa mai cin gashin kanta bisa wasu sharudda inda ma ya ce yin hakan hakki ne da ya rataya a kan wuyan duniya.
Isra'ila dai ta dakatar da shigar da kayan agaji na tsawon watanni uku a Gaza kafun daga bisani ta dawo da kwarya-kwaryansa a kwanan nan, kuma ko da a ranar Alhamis, ta bai wa mutane umurnin ficewa daga wasu yankunan arewacin na Gaza inda sojojinta ke luguden wuta ta sama da kuma ta kasa.