SiyasaArewacin Amurka
Amurka ta haramta ba da biza ga Nijar da wasu kasashe
December 17, 2025
Talla
Jamhuriyyar Nijar da Mali da Burkina Faso da kuma Sudan ta Kudu na daga cikin kasashen da Trump ya haramta wa al'ummarsu shiga kasar ta Amurka kama daga'yan yawon bude ido da dalibai da kuma 'yan kasuwa.
Katin bayani: Amurka ta soke bizar wasu 'yan kasashen ketare
Kafin daukar wannan matakin, Shugaba Trump ya sanya hannu kan kudurin haramta wa 'yan kasashen Afghanistan da Myanmar da Chadi da Jamhuriyyar Dimukuradiyyar Kwango da Equatorial Guinea da Eritrea da Haiti har ma da Iran da Libya da Somaliya da Sudan da kuma Yemen shiga kasar tun a watan Yunin 2025.
Hukumomin Washington DC sun sanar da cewa haramcin bada bizar zai fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Janairun 2026.