Amurka ta haramta wa marubuci Wole Soyinka shiga kasar
October 28, 2025
Fitaccen marubucin nan 'dan Najeriya da ya taba lashe lambar yabo ta Nobel Farfesa Wole Soyinka, ya sanar a Talatar nan cewa Amurka to soke bizar da ta ba shi a bara, tare shawartarsa da ya sake cike takardun neman wani izinin shiga kasar matukar yana da muradin kai ziyara.
Farfesa Soyinka ya nuna wa 'yan jarida wasikar da ofishin jakadancin Amurka na jihar Lagos ya aike masa, da ke bukatarsa ya mi ka fasfo dinsa don soke bizar a jiki.
A cikin shekarar 2016 marubucin ya yaga katinsa na shaidar izinin zama a Amurka wato green card, tare da ayyana sarayar da 'yancin da yake da shi na zama a kasar, a wani mataki na nuna adawa da zabar Donald Trump a matsayin shugaban Amurka a zangon mulkinsa na farko.
Karin bayani:Najeriya ta bijire wa muradin Trump na jibge mata bakin hauren Venezuela
A wani labarin kuma 'yan jarida a kasar Tunisia sun koka kan karuwar barazana da kuma matsin lamba da suke fuskanta daga hukumomin kasar, musamman ma jami'an tsaro, kamar yadda kungiyarsu ta The National Syndicate of Tunisian Journalists SNJT ta sanar a wannan Talata.
Kungiyar ta nuna damuwa da yadda ake dakile ayyukan mambobinta ta hanyar hantara da wulakanci da nuna wariya a cikin harkokin kasar, musamman yadda 'yan sanda ke haramta musu shiga kotuna, domin daukar rahoton shari'ar wadanda aka kama bisa banbancin akida ta siyasa da sauran matsaloli.
Kungiyoyin kare hakkin 'dan adam sun jima da nuna bacin ransu da yadda al'amura ke wakana a kasar da ta fuskanci tashin hankanli da tarzoma a dalilin boren al'umma na shekarar 2011.