1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amurka ta harbo jiragen Iran marasa matuka a mashigin Hormuz

Binta Aliyu Zurmi
June 13, 2026

Amurka ta ce ta kakkabo jiragen Iran marasa matuka da dama da ke shirin kai hari kan jiragen dakon mai a mashigin ruwan Hormuz a wannan rana ta Asabar.

Symbolbild Persischer Golf | US-Kriegsschiff USS Boxer auf Patrouille
Hoto: Cappello/Fotogramma/ROPI/picture alliance

Wannan matakin na zuwa ne sa'o'i bayan da bangarorin biyu suka ce ana dab da cimma yarjejeniyar kawo karshen yakin Gabas ta Tsakiya.

A jiya Juma'a ne firaministan Pakistan Shehbaz Sharif ya ce Amurka da Iran sun amince da kalaman da aka zayyana a yarjejeniyar sulhu da za ta kawo karshen yakin da aka fara a karshen watan Fabrairu.

Pakistan dai ta kasance mai shiga tsakani a tattaunawar da mika bayanai da kuma shawarwarin da aka cimma tsakanin bangarorin biyu a baya bayan nan.

Sharif ya wallafa a shafinsa na sada zumunta na X a ranar Juma'a cewa ba a taba samun lokacin da aka kai ga wannan gabar da ake kai a yanzu ba.

Bayanai daga bangarorin biyu da ke fada da juna sun nuna an sami gagarumin ci gaba.

Karin Bayani: Amurka ta yi ikrarin yin sulhu da Iran