Amurka ta janye sojinta daga Jamus bayan kin yakin Iran
May 2, 2026
Sakataren harkokin tsaron Amurka Pete Hegseth ya ba da umarnin janye dakarun sojin kasar dubu biyar da ke nan Jamus, sakamakon yadda dangantaka ke kara tsami tsakanin Amurka da kasashen Turai, sanadiyyar sabanin ra'ayi a kan yakin Iran.
Karin bayani: Alakata da Trump ba ta girgiza ba - Merz
Sanarwar da shelkwatar tsaron kasar ta Pentagon ta fitar ranar Juma'a, ta ce za a kammala kwashe sojojin daga nan zuwa shekarar 2027, a matsayin ramuwar gayya kan yadda aminanta na Turai suka ki mara mata baya a yakin Gabas ta Tsakiya, musamman ma batun bude mashigin Hormuz da karfin tuwo.
karin bayani: Duniya na yi wa Trump jaje bayan ya tsallake rijiya da baya
Shugaban Amurka Donald Trump ya fusata da kalaman da shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz ya furta cewa Iran ta kunyata Amurka a idon duniya, musamman ma kan yadda tattaunawar sulhunta yakinsu ke wakana.
Karin bayani: Tarayyar Turai ta ki goyon baya a yakin Amurka da Isra'ila a Iran
Haka zalika Mr Trump ya sanar da karin harajin kashi 25 cikin 100 ga motocin kasashen kungiyar tarayyar Turai EU da ake shigarwa Amurka, wanda zai fara aiki a mako mai kamawa, inda ya zargi kamfanonin motocin Jamus na Mercedes-Benz da BMW da tarwatsa ci gaban kasuwancin Amurkawa.