1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Amurka ta kaddamar da hari kan Isfahan

March 31, 2026

Amurka ta ce ta kai farmakin ne kan wani wuri da ake zaton an boye uranium da Iran ta inganta.

Amurka ta kai hari kan birnin Isfahan na Iran
Amurka ta kai hari kan birnin Isfahan na Iran Hoto: UGC/AFP

Wani hari da Amurka ta kai a tsakiyar birnin Isfahan da safiyar Talata ya haddasa gobara mai karfi da ta rika yaduwa zuwa wasu sassan birnin baya ga bakin hayaki da ya kaure sararin samaniyar binin.

 A lokaci guda kuma, Tehran ta kai hari kan wani jirgin dakon man fetur na Kuwait a cikin tekun Fasha.

Yakin Iran na fadada

Hare-haren sun nuna tsananin yaƙin da aka shafe wata guda ana gwabzawa bayan Amurka da isra'ila sun far wa Iran a ranar 28 ga Fabrairu.

Iran ta ci gaba da riƙe iko da mashigar Hormuz, inda ta rufe wannan muhimmiyar hanyar jigilar makamashi ta duniya, lamarin da ya jawo tashin farashin mai da rikicewar kasuwannin duniya.

Shugaban Amurka, Donald Trump, wanda ke cewa ana samun ci gaba a tattaunawar diflomasiyya domin tsagaita wuta, ya wallafa bidiyon harin da aka kai Isfahan.

Isra'ila ta kai sabbin hare-hare Tehran

Isfahan na ɗaya daga cikin wurare uku da sojojin Amurka suka kai wa hari a watan Yunin bara, kuma ana zargin cewa ana adana ko binne wani ɓangare na uranium da aka inganta a can.

A gefe guda kuma, Isra'ila ta ce wasu ƙarin sojojinta huɗu sun mutu a mamayar da take yi wa Lebanon, haka kuma wasu sojojin wanzar da zaman lafiya biyu na Majalisar Dinkin Duniyan sun mutu, lamarin da ya sa kwamitin tsaro na MDD ya shirya zaman gaggawa a yau Talata.