Sojojin Amurka sun hallaka wasu yan ta'adda a Somaliya
September 13, 2018Talla
Sanarwar ta kara da cewar an fara harin na hadin gwiwa ne tun cikin mako da ya gabata, a kauyen Mubaraak da ke yammacin birnin Mogadishu. Kasar Amurka dai na goyon bayan gwamnatin Somaliya a kan yaki da 'yan ta'dda, wadanda har yanzu suke rike da wasu yankunan kasar. A 'yan kwanakinnan dai mayakan na kungiyar Al-shabaab sun zafafa hare-haren kan fararen hula.