1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amurka ta kai wa Iran sabbin hare hare

Abdullahi Tanko Bala
July 20, 2026

Sojojin Amurka sun ce sun kaddamar da sabbin hare hare kan wasu cibiyoyi a Iran da ke zama kwana tara a jere suna kai hari cikin dare

Sojin Amurka yayin yaki da Iran a mashigin Hormuz
Sojin Amurka yayin yaki da Iran a mashigin HormuzHoto: SIPA/picture alliance

A cewar rundunar sojin Amurka a yankin Gabas Ta Tsakiya hare haren na da nufin dakushe tasirin Iran na iya kai hari kan jiragen ruwa a mashigin Hormuz.

A cewar kamfanin dillancin labaran Tasnim an ji karar fashewar abubuwa a arewacin birnin Tabriz mai tashar jiragen ruwa a gabar kogin Oman da Konarak a kudu maso gabashin Sistan-Baluchistan da sauran yankuna.

Kuwait ta ruwaito kakkabo wasu makaman masu linzami.

A halin da ake ciki kuma Tehran ta mayar da martani da kai hare hare kan kasashen da sansanonin sojin Amurka suke a yankin wadanda suka hada da Kuwait da Baharain da Qatar da kuma Jordan.