SiyasaAfirka
Amurka ta kakaba wa gwamnatin Sudan takunkumai
June 28, 2025
Talla
A cikin wata sanarwa da ta wallafa a jiya Juma'a, ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta tabbatar da cewa takunkumin na tsawon akalla shakara guda da aka labtawa Sudan din ya jibanci katse taimakon agajin gaggawa da kuma kayayyakin amfani gona.
Karin bayani: Gargadin yuwuwar kisan kare dangi a rikicin Sudan
A cewar Washington ta dauki wannan mataki ne saboda gwamnatin ta Sudan ta karya yarjejeniyar haramta yin amfani da makamai masu guba wadda aka amince da ita a watan Mayu na shekarar 1999.
A cikin watan Mayu da ya gabata ne dai Amurka ta zargi Sudan da yin amfani da harantattun makamai masu guba a cikin shekarar 2024, zargin fadar mulki ta Khartoum ta musanta saboda rashin gabatar da gamsassun hujjoji.