1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amurka ta kama mai kwarmata bayananta na sirri

April 14, 2023

Ta yiwu wani matashi dan Amurka ne ya kwarmata bayanan sirrin kasar dangane da yakin da ke faruwa kasar Ukraine. Hukumomi a Maurka sun kama wani mai shekaru 21 da ake zargi.

Hoto: WCVB-TV/AP/picture alliance

Bayan wallafe-wallafen wasu takardun da ke dauke da bayanan sirrin Amurka game da yakin da ke faruwa a Ukraine, hukumar bincike manyan laifuka ta Amurkar ta kama wani da take zargi.

Wanda aka kaman dai wani matashi ne mai shekaru 21, da ke aiki da rundunar sojin kasa, kamar yadda babban lauyan gwamnati Merrick Garland ya tabbatar.

Wasu hotunan bidiyo da kafofin watsa labaru suka yada, sun nuno yadda ake tasa keyar matashin mai suna Jack T, zuwa wata motar da ke shake da jami'an tsaro a gabashin birnin Massachusetts.

Kowane laifi guda da aka samu mutum da aikatawa da ya shafi kwarmata bayanan sirrin Amurka na iya kai mutum ga daurin shekaru 10 a gidan yari.