1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Amurka ta koka da sojin Sudan na hana shigar da agaji Darfur

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
February 26, 2024

Mutane kusan 700,000 ne suka tsallaka Chadi daga Sudan tun bayan barkewar rikicin a watan Afirilun bara tsakanin dakarun Janar Abdel Fattah al-Burhan da na jagoran RSF Mohamed Hamdan Dagalo kan neman madafun ikon Sudan

Hoto: Zohra Bensemra/REUTERS

Amurka da kuma masu aikin jigilar kayan agaji zuwa yankin Darfur sun koka da yadda sojojin Sudan masu biyayya ga tsagin Janar Abdel Fattah al-Burhan suka datse jigilar kayan agaji zuwa yankin yammacin Darfur.

Karin bayani:Kotun ICC ta ce an aikata laifin yaki a rikicin Sudan

Babban jami'in hukumar kula da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya Eddie Rowe ya shaidawa manema labarai cewa sojojin Sudan sun dakatar da shigar da kayan agaji daga Chadi, zuwa Darfur da ke hannun dakarun RSF na Mohamed Hamdan Dagalo.

Karin bayani:MDD ta ce an halaka mutane dubu goma sha biyar a yankin Darfur na Sudan

Ita ma Amurka ta bakin mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajenta Matthew Miller, ta nuna damuwa da wannan mataki na sojoji da ta ce zai shafi al'umma sosai.

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta duniya ta ce mutane kusan dubu dari bakwai ne suka tsallaka Chadi daga Sudan daga watan Afirlun bara zuwa yanzu, sakamakon barkewar yakin basasa tsakanin dakarun Janar Abdel Fattah al-Burhan da na jagoran RSF Mohamed Hamdan Dagalo kan neman madafun ikon Sudan.