Amurka ta kori shugaban hukumar leken asirinta na soji
August 23, 2025
Gwamnatin Amurka ta sanar da cewa ta kori shugaban hukumar leken asirin sojin kasar Laftanar Janar Jeffrey Kruse a jiya Juma'a, lamarin da ke zuwa bayan korar wasu manyan hafsoshin soji da Washington ta yi a watannin baya-bayan nan.
An sallami Laftanar Janar Jeffrey Kruse daga wannan mukami da yake rike da shi tun a farkon shekarar 2024 jim kadan bayan da ofishinsa ya fitar da wani rohoto da ke nunar da cewa hare-haren da Amurka ta kai wa tashoshin nukiliyar Iran a watan Yuni ya mayar shirin nukiliyar Teheran baya da shekaru da dama.
Karin bayani: Amurka ta kai hari kan cibiyoyin nukiliyar Iran uku
Wannan rahoto da jaridu suka yi ta yadawa ya fusata fadar mulki ta White House, domin ya yi hannun riga da ikirarin da shugaba Donald Trump ya yi na cewa hare-haren Amurka sun lalata tashoshin nukiliyar Iran ga baki daya.
Tun dai bayan dawowarsa kan garagar mulkin Amurka, shugaba Donald Trump ya kori manyan jami'ai da dama daga ma'aikatar tsaro ta Pentagon, inda ya fara da babban hafsan hafsoshin sojin kasar Charles Brown.