1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amurka ta kudiri aniyar kawo karshen yakin Sudan

Mahmud Yaya Azare
November 4, 2025

Amurka ta gabatar da kudirin neman tsagaita wuta a Sudan, lamarin da ke ci gaba da jawo martani mabanbanta daga bangarorin da ke gwabza yaki tun fiye da shekaru biyu

Amurka ta kudiri kawo karshen yakin Sudan
Amurka ta kudiri kawo karshen yakin SudanHoto: Ampersand

Kudirin tsagaita wutar na tsawon watanni uku da za a iya tsawaita shi har zuwa watanni tara, jakadan Amurka na musamma a nahiyar Afirka Massad Bulus ne ya sanar da hakan ga 'yan jarida, kudirin da ya kunshi barazana da jan kunne ga jagororin yakin na Sudan:

"Kowa ya ga yadda shugaba Trump ya yi fice wajen kawo karshen yake-yake da samar da zaman lafiya a duniya. Sudan ba za ta zamo waken suya ba. Don haka muke gargadin ga jagororin yakin Sudan da su gaggauta karbar wannan shirin. Domin a shirye muke mu samar da zaman lafiya a Sudan ko da tsiya ko da arziki. Wannnan kuma ita ce dama ta karshe da muke basu, idan basu yi amfani da ita ba, to za mu dauki wasu matakai na daban.”

 Wannnan kudirin na Amurka dai na zuwa ne, bayan da tarukan da aka yi ta yi a biranen Jiddah na Saudiya da Geneva na kasar Switzerland suka kasa kawo karshen yakin, ko ma cimma wata yarjejjeniyar da za ta bayar da dammar da gudanar da ayyukan a gaji a kasar da Majalisar Dinkin Duniya ke tabbatar da cewa, kusan rabin al'ummarta sun tsunduma cikin matsalar yunwa da rashin abinci mai gina jiki gami da fama da annobar Amai da gudawa a wasu yankunan.

Sansanin yan gudun hijira a KordofanHoto: Guy Peterson/AFP/Getty Images

Tuni dai ofishin gwamnatin sojin Sudan, ya sanar da gudanar da zaman majalisar tsaronsa don tattauna kudirin tsagaita wutar na Amurka, bayan da a baya yasha yin fatali da gayyatar da Amurkan ta yi masa na zama kan teburin shawara da yan tawaye don kawo karshen rikicin mulki da bangarorin sojin kasar ke yi da juna.

Sayyed Bashar Ja,arah,mai fashin baki kan siyasar Amurka a kasashen Afirka yayi bayani kan dalilin day a sanya gwamnatin Sudan a wannan karon tai gaggawar tarbar sabon kudirin na Amurka:

Zaman kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya kan rikicin SudanHoto: Manuel Elias/Xinhua/IMAGO

 "Mai yiwuwa kasancewar kudurorin da aka gabatar a baya, basu fito karara sun bayyana wa mahukuntan Sudan cewa, wannan rikicin ba batu bane na cikin gida da ya shafi kasar Sudan kadai ba. A yanzu Amurka ta nuna cewa a shirye take tayi taron dangi don murkushe duk bangaren da ke kokarin zama kangi ga samar da zaman lafiya a Sudan.”

A nata bangaren,tuni kungiyar yan tawaye ta RSF ta yi lalale maraba da wannan tayin na Amurka, yadda kakakin gwamnatin da suka kafa a yankin Darfur da suke kiranta gwamnatin gina tushen kasa, Ahmad Majbur ya wallafa a shafinsa na X cewa sun jima suna jiran manyan kasashen duniya sun nuna jan ido ga gwamnatin sojin Sudan da ke yin tutsu da duk wani tayin sulhuntawa da ake mata:

"Janar Al Burhan a shirye yake ya kone Sudan baki dayanta don ya ci gaba da zama kan mulki, don haka matakan lallama ba za su yi masa wani tasiri ba. Inda tun da fari,vduniya ta tashi haikan wajen matsa masa lamba, da tuni an kawo karshen wannan rikicin.”

Hoton tauraron dan Adam kan ta'asar yaki a SudanHoto: Vantor/AFP

Kafin wannan tayin na Amurka dai, sai da kawancen kasashe hudu da suka hada da Masar da Hadaddiyar Daular Larabawa da Saudiya da Amurka, suka gayyaci bangarorin da su zauna kan teburin shawara don warwre rikicin cikin lumana, amma bangaren rundunar sojin Sudan ta yi fatali da tayin, tana mai shan alwashin ci gaba da yakar yan tawayen har sai ta gama murkushesu da karfin tuwo.

Masharhanta dai, irin su Dr Butsainah Kaaram, ta cibiyar binciken lamuran Nahiyar Afurka da ke Masar na ganin cewa, akwai kyakkywar fatar samun nasarar sabon kudirin na Amurka a wannan karon:

"Amurka a yanzu tana da kwarin guiwar tirsasa wa gwamnatin Sudan yin aiki da kudirinta, sakamakon asarar baya bayanan da gwamnatin ta yi na birnin Alfasheer da barazanar da yan tawayen ke yi na sake kwace iko da karin yankuna. Haka nan kokarin da ta ke na hana masu kishin Islama dawowa kan mulki a Sudan, wadanda a yanzu suke taya dakarun gwamnati yaki da kuma hana kasar Iran yin tasiri a kasar, wacca itama a yanzu ta ke goyon bayan gwamnati, lamarin da kasashen Saudiya da Daular larabawa ke matukar yin adawa dashi.”

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani