1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amurka na son inganta lafiyar Kiristoci a Najeriya

December 21, 2025

Amurka ta ce ta kulla yarjejeniya da Najeriya domin karfafa tsarin kiwon lafiya, bayan da Shugaba Donald Trump ya zargi cewa a na yi wa Kiristoci kisan gilla a kasar.

Shugaban kasar Amurka, Donald Trump
Shugaban kasar Amurka, Donald TrumpHoto: Doug Mills/The New York Times/AP Photo/picture alliance

Gwamnatin Amurka ta ce ta kulla yarjejeniya da Najeriya domin karfafa tsarin kiwon lafiya. A karkashin yarjejeniyar ta tsawon shekaru biyu, Amurka za ta ba da tallafin kusan dala biliyan 2 don taimakawa wajen dakile yaduwar cutar HIV da tarin fuka da zazzabin cizon sauro da cutar shan inna, da kuma ba da kariya ga mata masu juna biyu da yara kanana.

Karin bayani: Amurka za ta hana masu kisan Kiristocin Najeriya biza

Ma'aikatar harkokin cikin gida ta Amurka ta ce yarjejeniyar tana mayar da hankali wajen tallafa wa cibiyoyin kiwon lafiya na Kiristoci. Yarjejeniyar da aka kulla na zuwa ne bayan da gwamnatin Najeriya ta yi kwaskwarima domin bayar da fifiko wajen kare rayukan Kiristoci, a cewar kakakin ma'aikatar harkokin cikin Amurka. A cikin watan Nuwanba ne, Shugaba Trump ya ce Amurka za ta dauki matakin soja kan Najeriya bisa zargin aikata kisan gilla kan Kiristoci. Amma Najeriya ta kara jadadda cewa ba a nuna tsangwama ga kowanne addini a kasar.

   

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW