1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaVenezuela

Amurka ta kwace wani jirgin dakon man Venezuela

December 21, 2025

Hukumar tsaron tekun Amurka tare da goyon bayan ma'aikatar tsaron kasar Pentagon, sun kama wani jirgin dakon mai a bakin tekun Venezuela.

Amurka ta kwace wani jirgin dakon man Venezuela
Amurka ta kwace wani jirgin dakon man VenezuelaHoto: DW

Amurka ta kama wani jirgin dakon mai a bakin tekun Venezuela  yayin da dangantaka ke kara tsami tsakanin kasashen biyu. Sakatariyar Ma'aikatar Tsaron Cikin Gida ta Amurka  Kristi Noem, ta ce Amurka za ta ci gaba da bin diddigin abin da ta kira haramtacciyar safarar man fetur.

Karin bayani:Venezuela:Matakin Amurka na toshe man fetur bai yi nasara ba 

Gwamnatin Venezuela karkashin shugabancin Nicolas Maduro, ta yi Allah wadai da kama jirgin man tare da bayyana hakan a matsayin fashi da ma garkuwa da mutane. Wannan shi ne karo na biyu da Amurka ta kama jirgin dakon mai a bakin tekun Venezuela, tun bayan da shugaban Amurka Donald Trump, ya bayar da umarnin hana zirga-zirgar, inda ya ce jiragen Amurka su kama duk wani jirgin dakon mai da ke shiga ko fita daga Venezuela.