Amurka ta nuna alamun sa ido kan tsagaita wuta a Ukraine
January 6, 2026
Shugabannin Turai da ke dasawa da Ukraine sun hadu da wakilan Amurka a birnin Paris don tattauna makomar tsaron kasar. Tuni ma daftarin sanarwar hadin gwiwa ya ce Amurka na shirye wajen jagorantar sa ido da kuma tabbatar da tsagaita wuta a Ukraine idan aka cimma yarjejeniyar zaman lafiya da Rasha. Sannan daftarin ya kara da cewa Washington za ta yi alkawarin tallafa wa rundunar sojojin kasa da kasa da Turai za ta tura a Ukraine domin hana Rasha sake kai hari bayan tsagaita wuta.
Karin bayani: Shawari 28 na sasanta Ukraine da Rasha
Ana sa ran rundunar za ta samar da tsaro da kwanciyar hankali ga Ukraine ta sararin samaniya da teku da ta kasa, yayin da za ta taimaka wajen sake ginawa da karfafa rundunar sojojin Ukraine. Amurka za ta ba da gudummawarta a fannin leken asiri da dabaru da sufuri, tare da alkawarin tallafa wa rundunar idan Rasha ta sake kai hari.
Karin bayani: Kokarin Turai na kawo karshen yakin Ukraine
Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya karbi bakuncin taron da ake kira na kawayen Ukraine, ciki har da shugabannin Turai, da shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky da wakilan Amurka, da nufin daukar matakan kare Ukraine da kuma tabbatar da zaman lafiya mai dorewa.