Amurka ta sake bijire wa kokarin kawo karshen yaki a Gaza
September 19, 2025
Talla
Kasar ta Amurka ce dai kadai ta kada kuri'ar adawa, yayin da sauran kasashe 14 ciki har da Rasha da China da Burtaniya da Faransa da sauran mambobin wucin gadi 10 suka goyi bayan kudurin.
Kudurin ya nuna damuwa matuka kan yunwar da ake fama da ita a Gaza, tare da kira ga gwamnatin Isra'ila ta gaggauta janye duk wani hani ga shigar da agajin jinkai zuwa Gaza.
Wannan dai shi ne taro na 10,000 na kwamitin sulhun tun bayan kafa ta shekaru 80 da suka gabata, a cewar Majalisar Dinkin Duniya,.
Wakiliyar Amurka, Morgan Ortagus, ta kare wannan mataki na adawa da hujjar cewa kudurin da ta kira “maras karbuwa” da ke mara wa kungiyar Hamas baya.