1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Amurka ta sanyawa jagoran RSF na Sudan takunkumi saboda yaki

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
January 7, 2025

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya ce hare-haren RSF na zama na kabilanci, inda ta fi kashe wasu kabilu da gayya, tare da yi wa matansu fyade.

Motocin kayan agaji a Sudan
Hoto: Mohamed Iyssa/picture alliance

Amurka ta kakaba wa jagoran dakarun RSF da ke yaki da sojojin gwamnatin Sudan takunkumi tare da masu mara masa baya, bayan da ta ce ya jagoranci aikata laifin kisan kiyashi ga dubban mutanen Sudan, tare da raba miliyoyi da muhallansu.

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya ce hare-haren RSF na zama na kabilanci, inda suka fi kashe maza da mata na wasu kabilu da gayya, tare da yi wa matansu fyade da ma sauran nau'ikan cin zarafi.

Karin bayani:Harin RSF a yankin Darfur na Sudan ya halaka mutane 12

Haka zalika dakarun RSF na kashe mutanen da ke tserewa yakin, dalilin sanya wa shugabanta Mohamed Hamdan Dagalo takunkumin hana shi shiga Amurka da kuma kame kadarorinsa da dukiyoyinsa da ke kasar.

Karin bayani:Wani sabon hari a kasuwa ya halaka rayuka a Sudan

Sama da watanni 18 da barkewar yakin basasar, wanda ya raba mutane miliyan 12 da gidajensu, baya ga dubban da suka halaka, har ma Majalisar Dinkin Duniya ta ayyana halin da al'ummar ke ciki a matsayin yanayin jin kai mafi muni a duniya.