1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaArewacin Amurka

Amurka ta shirya wa Carter jana'izar ban girma

December 30, 2024

A daidai lokacin da shugabannin kasashe ke ci gaba da aike wa da sakon ta'aziyya ga Amurka, fadar White House ta sanar da ranar 9 ga watan Janairu 2025, a matsayin ranar da za a yi wa Jimmy Carter jana'izar ban girma.

Tsohon Shugaban Amurka Jimmy Carter
Tsohon Shugaban Amurka Jimmy CarterHoto: Abaca Olivier Douliery/dpa/picture alliance

Tuni dai aka yi kasa-kasa da tutocin kasar ta Amurka a dukkan hukumomi da ma'aikatun gwamnati da ke fadin kasar a matsayin makokin bankwana da gwani kuma shugaban kasar mafi dadewa Jimmy Carter wanda ya rasu a jiya Lahadi yana da shekaru 100.

Karin bayani:Tshohon shugaban Amurka Jimmy Carter ya mutu yana da shekaru 100 

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres da shugaban kasar Isra'ila Isaac Herzog da shugaban kasar China Xi Jinping na daga cikin shugabannin da suka nuna alhini na mutuwarta Carter. Daga can kuwa fadar Vatican, Fafaroma Francis ya bayyana marigayin a matsayin mai tsoron Allah da kuma kishin addini.