1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amurka ta tsananta takunkumi kan kasar Iran

February 25, 2026

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya kara tsananta takunkumi kan Iran a ranar Laraba, a cikin wata tattaunawa da ya kira "matsin lamba mafi girma," a daidai lokacin da ake shirin tattaunawa mai muhimmanci a Geneva.

 Donald Trump da Ayatollah Ali Khamenei
Donald Trump da Ayatollah Ali Khamenei Hoto: Andrew Caballero-Reynolds/AFP

Sabbin takunkumin sun shafi fiye da mutane 30, da hukumomi da jiragen ruwan dakon kaya da ake zargin su na taimakawa siyan mai ba bisa ka'ida ba, da kuma harkokin kera makamai na Iran. Trump ya sha yin barazanar kai hari idan Iran ba ta cimma yarjejeniya kan shirin nukiliyarta ba.

A gefe guda, Iran ta mayar da martani ta na sukar maganganun shugaban Amurka, daga kiran su karya tsagwaronta zuwa nuna cewa tattaunawar na iya kawo yarjejeniya ta hanyar diflomasiyya

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Amurka ke tura jiragen sama da na ruwa mafi yawa zuwa Gabas ta Tsakiya cikin shekaru da dama, yayin da Iran ke fama da sabuwar zanga-zangar lumana da rikice-rikice a cikin gida bayan zanga zangar gama gari a watan da ya gabata.