1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amurka ta yi fito na fito da Chaina kan kudin haraji

Abdullahi Tanko Bala SB
April 9, 2025

Lamura suna kara dagulewa tsakanin kasashen Amurka da Chaina na kakaba kudin fiton kayayyaki kan juna tun lokacin da Shugaba Donald Trump na Amurka ya fara saka kudin fito mai tsauri kan kasashen duniya.

Kasuwar hannun jari a Jamus
Kasuwar hannun jari a JamusHoto: Martin Meissner/AP/picture alliance

Shugaban Amurka Donald Trump ya jefa kasar cikiin yakin cinikayya da sauran kasashen duniya tare da karin harajin da yake kwan-gaba kwan-baya tare da haifar da yanayi na rashin tabbas. Trump ya ce karin harajin martani ne don daidaita cinikayya da kasashe. Masana tattalin arziki dai sun yi gargadin cewa ramuwar gayya kan karin haraji zai sauya kyakkyawar huldar cinikayya da kuma yarjejeniyar da aka dade ana aiwatarwa. Yanzu haka Shugaba Trump ya kara yawan harajin kudin fiton kan Chaina zuwa kaso 125 cikin 100, tare da dakatar da fara aiki da na sauran kasashen duniya zuwa kwanaki 90 masu zuwa (watanni uku).

Karin Bayani: Yakin kasuwanci tsakanin China da Amurka ya fara gadan-gadan

Kasuwar hannun jari a AmurkaHoto: Angela Weiss/AFP/Getty Images

Trump dai ba bako bane wajen kakaba haraji. A wa'adin mulkinsa na farko ya kaddamar da yakin cinikayya musamman da Chaina inda ya dora musu haraji akan galibin kayyayakinsu. Beijin ta mayar da martani da dora nata harajin kan kayayyakin Amurka kama daga kan kayan marmari zuwa motoci da na'urori da Amurka ke shigar da su kasar.

A martaninta China ta ci alwashin yin karin kashi 84 cikin dari akan kayayyakin Amurka, matakin da zai fara aiki daga 10 ga watan Afrilu.A waje guda dai Trump ya yi amfani da barazanar karin haraji wajen tilasta wa Amurka da Mexico sake tattaunawa kan yarjejeniyar cinikayya ta arewacin Amurka wadda ake kira yarjejeniyar Amurka-Mexiko da Kanada ta 2020.

Kayayyaki a tashar jiragen ruwan AmurkaHoto: Charly Triballeau/AFP

Masana tattalin arziki dai sun yi kashedin cewa lamarin zai iya haifar da mummunan sakamako kan kasuwanci da tattalin arziki a duniya baki daya ´tare da haifar da tsadar rayuwa ga al'umma. Bugu da kari Trump ya yi alkawarin karin haraji da kashi 200 kan barasar da ake shigar da ita daga kasashen Turai idan kungiyar tarayyar Turan ta aiwatar da shirin da ta sanar a baya na karin kashi 50 cikin dari na barasar Amurka.

A halin da ake ciki kungiyar tarayyar Turai ta kada kuri'ar karin harajin dala biliyan 23 akan kayayyakin da ake shigar da su daga Amurka. Da yake tsokaci shugaban gwamnatin Jamus mai jiran gado Friedrich Merz ya ce Jamus na nan daram a kan kafafunta.

Kayayyaki a tashar jiragen ruwan AmurkaHoto: Mario Tama/Getty Images/AFP

Ita ma kasar Spain da ta ke martani kan karin harajin Trump ta ce za ta karfafa hulda da China don biyan bukatun al'umarta da kuma kungiyar tarayyar Turai. Ministan ayyaukan gona na kasar ta Spain Luis Planas ya  yi watsi da gargadin Amurka wadda ta yi kashedin cewa kasar za ta dandana kudarta idan ta sake ta kulla alaka da nahiyar Asia. Sai dai Jakadan Amurka kan cinikayya Ambasada Jamieson Greer ya ce yana ganin akwai wata dama ta ragin haraji tsakanin Amurka da sauran kasashe don dage shingen cinikayya. Sai dai kuma a daya bangaren kasuwar hannayen jari ta shiga tangal-tangal tun bayan da Trump ya shiga takun saka kan yakin cinikayya da kasashe.