1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

AMURKA TAYI ALKAWARIN TAIMAKON KASAR SUDAN.

September 24, 2004

MINISTAN HARKOKIN WAJEN AMURKA COLIN POWELL LOKACIN DAYA KAI ZIYARAR AIKI SUDAN.

Hoto: AP

A kokarin da kungiyyar kasashen nahiyar Africa keyi na tabbatar da tsaro da kuma dukiyoyin mutanen yankin Darfur na kasar Sudan,yan majalisar dokokin Amurka sun yarda da kudirin samar da dalar Amurka Miliyan 75 a matsayin tallafi ga kungiyyar don tunkarar wan nan gagarumin aikin.

Kafin dai zartar da wan nan kudiri yan majalisar dokokin na Amurka sun gudanar da wasu yan gyare gyare a matakin da shugaba Bush ya gabatar na ware kudin tallafi daga Amurka izuwa wasu kasashe na duniya a cikin kasafin kudin shekara ta 2005.

A cewar wani sanata dan jamiyyar demokrat daga jihar new jersey,mai suna Jon Corzine,cewa yayi majalisar dokokin Amurka a shirye take tayi duk iya bakin kokarin ta wajen ganin an samu kwanciyar hankali a yankin na darfur.

Sanatan yaci gaba da cewa rahotanni da suka iske su ya nunar a fili cewa mutane a yankin na Darfur dubu hamsin ne suka shekara lahira a tsawon watanni goma sha tara,kana a daya hannun wasu miliyan daya da digo uku sukayi kaura don ceton rayukan su,kana a daya wajen kuma wasu miliyan biyu a yanzu haka suna bukatar taimakon kayayyakin agaji.

Sanatan yaci gaba da cewa bisa hakan ne majalisar dokokin ta Amurka ta zartar da umarnin,ware wadan nan kudade don karawa kungiyyar hadin kann nahiyar african karfi na gudanar da aikin kiyaye zaman lafiya a yankin na Darfur yadda ya kamata.

Har ila yau a daya waje kuma tarayyar Nigeria da a yanzu haka ke jagorancin shugabanin kungiyyar ta Au na nan na tunanin samun dalar amurka dari biyu daga hannun kasashe masu hannu da shuni don gudanar da aikin kiyaye zaman lafiya yadda ya kamata a yankin na Darfur.

A yanzu haka dai bayanai sun nunar a fili cewa kungiyyar ta Au ta shirya tura dakarun kiyaye zaman lafiya na kungiyayyar zambar dubu biyar,izuwa yankin da akace ana cin kashin mazauna yankin ta hanyar kashe su kamar kiyashi a kasar ta Sudan.

A sabili da irin cin kashin dake gudana a yankin na Darfur,tuni mdd da kungiyyar tarayyar Turai ta soki lamirin gwamnatin kasar ta sudan da nuna halin ko in kula game da shawo kann wan nan rikici ta hanyar lumana.

Bisa hakan kungiyyar tarayyar Turai ta bukaci mdd data duba yiwuwar tura dakarun ta izuwa yankin na darfur don gudanar da aikin kiyaye zaman lafiyar.

Bisa kuwa wadan nan korafe korafe,tuni gwamnatin kasar ta Sudan ta fito fili ta kalubalanci wan nan mataki da mdd ke kokarin dauka da cewa wan nan matsalace ta cikin gida a don haka zatayi duk abin da yaka mata don kawo karshen wan nan tashe tashen hankula da ake fuskanta a kullum ranar allah ta,ala a yankin na Darfur.

Ibrahim Sani.