SiyasaAfirka
Amurka za ta bai wa Sudan agajin Dala miliyan 100
April 14, 2024![](https://static.dw.com/image/65000912_800.webp)
Talla
Hukumar raya kasashe ta Amurka USAID, za ta bai wa Sudan agajin Dala miliyan 100, don tallafawa al'ummar da yakin basasa ya daidaita.
Karin bayani:'Yan Sudan suna fatan kawo karshen yaki
Wannan na cikin sanarwar da shugabar hukumar Samantha Power ta fitar, in ji kamfanin dillancin labaran Reuters, a daidai lokacin da yakin zai cika shekara guda cif da barkewarsa a ranar Litinin, 15 ga wannan wata na Afirilu.
Karin bayani:Amurka na shirin kawo karshen yakin Sudan
Al'ummar Sudan sun fada cikin matsanancin yanayi na yunwa mafi muni a duniya, sakamakon yaki kan madafun iko tsakanin sojojin da ke biyayya ga Janar Abdel Fattah al Burhan da dakarun RSF da ke karkashin Mohamed Hamdan Dagalo.