1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaUkraine

Blinken na ziyarar ba zata a Ukraine

September 6, 2023

Sakataren harkokin wajen Amurka ya isa birnin Kiev na Ukraine inda ya fara wata ziyarar ba zata a daidai lokacin da kasar ta canja ministanta na tsaro.

Amurka za ta bai wa Ukraine sabon tallafiHoto: Brendan Smialowski/REUTERS

A yayin ziyarar jami'in diflomasiyan na Amurka Antony Blinken, ya yi albishir ga hukumomin Kiev, na ba wa kasar tallafin da ya kai dala biliyan guda domin ci gaba da kare kanta daga dakarun mamaya na Rasha.

Karin bayani: Kawayen Ukraine za su ba ta jiragen yaki

Nan gaba kadan mista Blinken zai gana da shugaba Volodymyr Zelensky da kuma takwaransa  Dmytro Kouleba domin yin bitar nasarorin da Kiev ta samu bayan farmakin da ta kaddamar yau da watanni biyu domin karbe iko da wasu yankunan kasar da ke karkashin mamaya.

Karin bayani: Zafafa harin Rasha a Ukraine

Tuni dai Moscow ta yi martani kan ziyarar ta Blinken tana mai zargin Amurka da fakewa da sunan Ukraine domin yin yaki da ita, har ma ta kara da cewa wannan tallafi na Amurka ba zai kawo mata cikas ba kan muradinta a kan Ukraine.