Amurka za ta hana masu kisan Kiristocin Najeriya biza
December 4, 2025
Amurka ta ce za ta tsananta wa 'yan Najeriya da iyalansu da ake zargin suna da hannu a kashe-kashe ko tashin hankali kan Kiristoci wajen samun biza.
Wannan mataki na zuwa ne bayan sukar da Shugaba Donald Trump ya yi a kan rikicin addini a Najeriya, har ma ya umarci ma'aikatar tsaro ta Pentagon da ta fara duba yiwuwar daukar matakin soja, saboda yi wa Kiristoci kisan gilla a Najeriyar.
Sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio ya ce kasarsa na daukar mataki kan hare-haren da ’yan ta’adda da kungiyoyin makiyaya da sauran masu tayar da husuma ke aikatawa, tare da cewa sabon matakin ya yi daidai da sabuwar manufar shige da fice ta kasar Amurka.
Matakin Amurka na zuwa ne bayan shekaru na rikicin tsaro a Najeriya da Shugaba Donald Trump ke alakantawa da kisan Kiristoci da masu tsattsauran ra’ayin addinin Islama ke aikatawa.