1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaLatin Amurka

Mu za mu ja ragamar man Venezuela har abada - Amurka

Abdoulaye Mamane Amadou
January 8, 2026

Shugaban Donald Trump ya sha alwashin cewar Amurka za ta jan ragamar sayar da man kasar Venezuela har abada da ma yadda ake amfani da kudaden da aka samu daga cinikin man.

Shugaba Donald Trump na Amurka
Shugaba Donald Trump na Amurka Hoto: Alex Brandon/AP Photo/dpa/picture alliance

Amurka ta sha alwashin jan ragamar sayar da man kasar Venezuela har abada, tare da yanke shawarar yadda ake amfani da kudaden da aka samu daga cinikin man. Wannan na zuwa ne bayan da Amurka ta kwace jiragen dakon man Venezuelan guda biyu a Tekun Atlantika a ranar Laraba.

Za a rika ba wa Amurka gangar mai dubu 50 

Tun da fari dai Shugaba Trump ya ce gwamnatin rikon kwarya a Venezuela za su rika bai wa Amurka akalla gangar mai dubu 50, Wahsington din na kuma matsa lamba kan kulla yarjejeniya da Caracas don karkatar da danyen mai da take shirin sayar wa China da ya kai dala biliyan 2.

Martanin kasashen duniya kan matakin Amurka

China, wacce ke kan gaba wajen sayen man Venezuela, ta Allah wadai da matakin tanaa mai cewa zalunci ne da yunkurin haaifar da matsalar makamashi a duniya, Beijin ta ce za ta bi kadunta da ke Caracas, ana ganin wannan lamari na iya kara haifar da tsananin rikici tsakanin Amurka da China kan ikon makamashi da tasiri a Latin Amurka.

Ya farashin danyen mai yake a kasuwar duniya

Labarai daga kasuwannin duniya sun nuna cewa farashin mai ya sauka a wasu lokuta sannan ya dawo, yayin da masu zuba jari ke nazarin yadda wannan rikici zai shafi kasuwannin makamashi.