An ƙaddamar da yaƙin neman zaɓe a ƙasar Senegal
February 5, 2012Talla
Haɗin gwiwar jam'iyyun adawar waɗanda ake kiran da sunan M23 wanda suka haɗa da jam'iyyun siyasa guda takwas da kuma ƙungiyoyin fara hula na gudanar da wani gamgami a birnin Dakar. 'Yan adawar waɗanda suka ƙulla ƙawance domin tsayar da ɗan takara ɗaya, na da zunmar hanna shugaba Abdoulaye Wade wanda ke bisa gadon mulkin kusan shekaru 12 tsayawa zaɓen. Abdoul Azizi Diop shi ne kakakin ƙungiyar ta M23, yace maza da mata na wannan ƙungiya za su yi yunƙurin hanna Abdoulaye Wade gudanar da kampe saboda ba shi da hurumin yin farfagandin. To amma rahotannin da ke zo mana na cewar shi ma shugaba Wade ɗin na gudanar da na sa gangamin a garin Macke wanda ke a gabashin ƙasar.
Mawallafi : Anbdourahamane Hassane
Edita : Mohammad Nasiru Auwal