An ƙara samun mai Ebola a Amirka
October 15, 2014Jami'an hukumar kula da lafiyar al'umma a jihar Texas da ke Amirkan sun bayyana cewar ita ma wannan jami'ar jinyar ta biyu na daga cikin waɗanda suka kula da ɗan asalin Laberiyan nan Thomas Eric Duncan da ya rasa ransa a Amirkan sakamakon cutar ta Ebola. Tuni dai aka keɓance wannan jami'ar lafiyar a asibitin Dallas da ke Texas ɗin Amirkan, tare kuma da mayar da hankali wajen kula da duk waɗanda suka yi mu'amala da ita domin tantancewa ko suma sun kamu da annobar cutar Ebolan da ta addabi duniya. Kawo yanzu dai cutar ta hallaka sama da mutane 4,400 a ƙasashen da ta ɓulla a yankin yammacin Afirka, inda ƙasar Laberiya tafi ko wacce ƙasa yawan masu ɗauke da Ebolan, dama waɗanda suka mutu sakamakon cutar.
Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Abdourahamane Hassane