1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An ƙiƙiro sabbin na'urorin kashe gobarar daji a ƙasar Girka

YAHAYA AHMEDAugust 24, 2006

A yunƙurin da ake yii na shawo kan gobarar daji a duniya, masana kimiyyan jami'ar fasaha ta birnin Athens a ƙasar Girka, sun ƙiƙiro wasu fasahohi na gano tushen gobarar dajin kafin ma ta yaɗu ta fara haddasa ɓarna.

Masana'antar samad da makamashi a birnin Athens na ƙasar Girka
Masana'antar samad da makamashi a birnin Athens na ƙasar GirkaHoto: AP

Shirin na yau zai yi nazarin ƙoƙarin da ake yi ne a sassa daban-daban na duniya don shawo kan gobara da wutar daji, waɗanda ke barazana ga halin rayuwar ɗimbin yawan jama’a a ko wace shekara. A yankunan kudancin Turai da Asiya da Amirka da kuma Austreliya ne gobarar dajin ta fi aukuwa. Masana kimiyya a ƙasar Girka, ɗaya daga cikin ƙasashen da suka fi fama da wannan matsalar a nahiyar Turai, sun ƙiƙiro wata sabuwar fasaha don gano tushen gobarar kafin ma ta yaɗu ta fara ɓarna. A jami’ar birnin Athens, an yi gwajin waɗannan na’urorin, waɗanda ke sanad da ’yan kwana-kwana ɓarkewar duk wata gobarar daji a cikin lokaci, kafin al’amura su taɓarɓare.

A ƙasar Girkan dai an sha samun gobara a dazuzzuka a lokacin bazara. Wutar dai na haddasa ɓarna ga muhalli da dabbobi da ma kadarori da rayukan jama’a. Jami’an kashe gobaran ƙasar dai na zargin ’yan ɓata gari ne a galibi da ta da gobarar da gangan.

Sabbin na’urorin da masana kimiyyan suka ƙiƙiro, za su iya sanad da cibiyoyin kashe gobarar ne da dai an sami bambancin zafi a wani yanki. An kakkafa na’urorin ne a kan itatuwa a dazuzzukan da ke da kasadar ɓarkewar gobara. To dukkansu kuma na da ma’aunin zafi. A ko yaushe, suna aikewa da matsayin zafin yanayi ga na’urori masu ƙwaƙwalwa a tashoshin ’yan kwana kwana. To da an sami wani sauyi na hauhawar zafi, sai su yi ta gangami su kuma bayyana inda lamarin ya auku. Kai tsaye sai rukunan ’yan kwana kwana su tinkari gun da motocinsu da kuma jiragen sama ma masu saukar ungulu da aka ƙera musamman don kashe gobarar. Farfesa Vassilis Veskoukis, shugaban ƙungiyar masana kimiyyan da suka ƙikiro na’urorin ya bayyana yadda na’urorin ke aiki:-

„Da wannan fasahar, muna iya sanin yadda yanayin zafi yake a ko yaushe a dazuzzukan. Da zarar gobara ta barke kuma, muna iya gane hakan. Fasahar dai na da fa’ida musamman a yankunan da ke da dazuzzuka masu fadin gaske. Tana iya nuna mana yadda gobarar ta barke. Idan muka ga cewa an sami ɓarkewar gobara a wurare biyu ko uku a lokaci ɗaya, to shakka babu, mun san cewa ta da gobarar aka yi da gangan. Saboda na’urorin, muna iya gano inda ake gobarar, mu ɗau kuma matakan shawo kanta kai tsaye.“

Na’urorin na kuma nazarain yanayin sararin samaniya. Hakan na iya bamu damar yin hasashe game da yankunan da gobarar za ta iya ɓarkewa saboda fatara. To da waɗannan alƙaluman ne muke tanadin motoci da jiragen saman kashe gobara, mu kuma girke su kusa da inda muke hasashen cewa gobarar za ta iya aukuwa. Yanzu dai gwajin wannan fasahar aka yi. Ko za a iya yaɗa ta a duk faɗi ƙasar Girkan? Kuma nawa za a kashe a kan aikin? Game da waɗannan tambayoyin dai Farfesa Veskoukis ya bayyana cewa:-

„A halin yanzu ba mu da aƙaluman kuɗaɗen da za a kashe kan waɗannan ayyukan. Kawo yanzu dai gwaji kawai muka yi. Sabiili da haka ba za mu iya ba da lissafin kuɗin da za a kashe wajen yaɗa fasahar ba tukuna. Amma bisa gwajin da muka yi, za mu iya hasashen cewa, ba za a kashe maƙudan kuɗaɗe fiye da kima ba wajen gudanad da aikin. Kuma ba ko’ina ne za a kakkafa na’urorin ba. Za a sanya su ne inda muka san ba za a iya tura jami’an kula da dazuzzuka a ko yaushe ba.“

A halin yanzu dai an kashe kimanin Euro miliyan 2 da rabi wajen ƙirƙiro da kuma inganta waɗannan na’urorin. Gwajin da aka yi kuma, an taƙaita shi ne a yankin Nea Pendeli kusa da birnin Athens a kan wani filin daji mai faɗin hekta 40, inda a shekarun baya, aka yi ta samun ɓarkewar gobara. Farfesa Veskoukis ya ce kawo yanzu dai ba a sami wata matsala a gwajin da aka yi ko kuma da na’urorin ba:-

„Mun ɗan huskanci wata matsala inda aka kakkafa falwaya don jan wutar lantarki, amma mun shawo kanta. Tun daga wannan lokacin, na’urorin na aiko mana da duk alƙaluman da muke bukata musamman game da zafin yanayi. Hakan dai ya sa mun iya ci gaba da aikinmu har zuwa ƙarshensa.“

Ƙasashen Turai da dama da wasu kamfanoni masu zaman kansu na Amirka sun nuna sha’awa ga wannan fasahar. Kazalika wasu ƙasashen Asiya da kuma Austreliya ma sun nemi ƙarin haske kan fasahar. Idan dai aka bunƙasa ta aka kuma inganta ta don ta dace da bukatun ƙasashen ƙetare, fasahar za ta iya janyo wa ƙasar Girka wata gagarumar fa’ida a huskar cinikin ƙetare. Farfesa Veskousis dai na kyautata zaton cewa fasahar za ta iya aiki a ko’ina:-

„Ina fata za mu iya amfani da ita a ko’ina don yaƙan gobara a daidai lokacin da ta barke, kafin ma ta iya haddasa wata ɓarna. Za ta kuma iya bayyana mana tushen gobarar, ko da gangan aka ta da ita, ko kuma ta taso ne saboda dalilan yanayi. Idan an tabbatad da haka, to sauran matakan da za a ɗauka dai sun dogara ne kan mahukuntan ƙasa.“