1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

An afka wa 'yan adawa a Tanzaniya

September 4, 2021

'Yan sanda a Tanzaniya, sun kama mutane da dama a yankin kasar da jam'iyyar adawar nan ta Chadema ke da rinjaye. Hakan na zuwa ne bayan kama shugaban adawar kasar.

Tansania Daressalam Polizeieinsatz nach Gerichtsurteil
Hoto: DW/S. Khamis

Sabon matakin 'yan sandan na Tanzaniya, ya zo ne sakamakon yadda wasu daga yankin ke kiraye-kirayen sake fasalta tsarin mulkin kasar.

Kamen na yau Asabar, ya shafi wasu mutum tara da aka ce su ne suka kitsa gangamin, wanda suka ce kokari ne na kunna wutar kiyayya a kasar  ta Tanzaniya.

Shugaban 'yan sandan kasar, ya ce ba za su nade hannu suna kallon wasu na kokarin tayar da husuma a kasar ba.

A baya-bayan nan ma dai gwmanatin Shugaba Samia Suluhu Hassan, ta kama jagoran adawar kasar Freeman Mbowe, wanda aka zarga da laifin ta'addanci.