Habasha: Laifukan yaki kan fararen hula
November 3, 2021Wannan dai na kunshe ne cikin wani rahoton hadin gwiwa da ofishin Kwamitin Kare Hakkin dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya da kuma tsarin dokokin kare hakkin dan Adam na kasar Habasha suka bayar a Geneva. Hakan dai ya biyo bayan wani bincike da suka gudanar, inda suka bayyana cewa an aikata kisan ba gaira da fyade da musgunawa da cin zarafi da azabtarwa a kan fararen hula. Rahoton ya nunar da cewa sojojin gwamnatin Habashan da na makwabciyarta Iritiriya da kuma sojojin mayakan yankin Tigray TPLF da kawayensu ne suka aikata wadannan munanan ayyukan a yakin kasar da ke yankin Kahon Afirka da yaki ci yaki cinyewa. Mayakan na TPLF dai na ci gaba da samun nasara a kan dakarun gwamnati, abin da ya sanya mahukuntan Habashan saka dokar ta baci tare da bukatar al'umma su dauki makamai domin su kare kansu daga mayakan na TPLF.