1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Iran ta aiwatar da hukuncin kisa kan dan jarida

December 12, 2020

Rahotannin da ke fitowa daga Iran na nuna cewa hukumomin kasar sun zartar da hukuncin kisa ga dan jaridar nan da ke sukar manufofin gwamnati Ruhollah Zam.

Iran Journalist Ruhollah Zam
Hoto: Ali Shirband/AP Photo/picture alliance

Tun da farko dai mahukumtan na Iran sun kama shi da laifin zama kanwa-uwar-gami a zanga-zangar da aka yi wa gwamnati a shekara ta 2017.


Bayan da dan jaridar ya yi ta kauce-kauce domin tsira da rayuwarsa hukumomi sun kama shi har ma a shekarar da ta gabata kotun kolin kasar ta amince da aiwatar da hukuncin kisa a matsayin ladabtarwa ga laifin da suke ganin ya aikata wa kasar. Jaridar Amadnews ta dan jaridar dai nada mabiya fiye da miliyan daya a shafukan sada zumunta.