Najeriya ta amince da sake fasalin harkokin mai
July 1, 2021Majalisar dokokin Najeriya ta amince da dokar sake fasalin harkokin man fetir, bayan kwashe shekaru da dama ana jan kafa a kanta, dokar ta samar da sauye-sauye a harkar man fetir din Najeriya tare da bai wa sashen da ake hako mai kaso na musamman domin gudanar da aiyukan ci gaba.
Majalisun guda biyu na dattawa da wakilai, sun kafa tarihi inda suka amince da dokar. Kodayake dokar na da kashi 318 amma sassan da suka yi magana na samar da kaso daga ribar da kamfanonin mai za su samu don bai wa al'umman da ake samar da man da ma wadanda ake fafutukar nemansa ne suka fi jan hankali.
A majalisar tarayya kashi biyar aka amince da a ba su abin da ya nuna sai an yi taro a tsakanin majalisun biyu don cimma matsaya.
A yanzu ya rage majalisun biyu su samu daidaito kafin aikawa da dokar zuwa ga shugaban kasa don ya sanya mata hannu.