An amince da kwamitin yi wa kundin mulkin Masar kwaskwarima
February 6, 2011![](https://static.dw.com/image/6429529_800.webp)
Sakamakon matsin lamba daga zanga-zangar da aka shafe kusan makonni biyu ana yi a Masar, gwamnatin ƙasar ƙarƙashin shugaba Hosni Mubarak a karon farko ta fara tattaunawa da 'yan adawa. A wannan Lahadi dai a birnin Alƙahira, mataimakin shugaban ƙasa Omar Suleiman ya gana da wakilan ƙungiyar 'yan'uwa Musulmi wadda a hukumance an haramta ayyukanta da kuma sauran 'yan siyasa na ɓangaren adawa, inda suka tattauna game da makomar ƙasar. Wani kakakin gwamnati ya rawaito cewa a gun taron an amince da kafa wani kwamiti a cikin wata guda, wanda zai duba irin gyare gyaren da za a yi wa kundin tsarin mulkin ƙasar. To sai dai duk da haka har yanzu ana ci-gaba da zanga-zanga a tsakiyar birnin Alƙahira da ma wasu birane inda ake kira ga shugaba Mubarak da ya sauka daga kan karagar mulki.
A kuma halin da ake ciki a karon farko cikin mako guda an buɗe bankuna a faɗin ƙasar baki ɗaya.
Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Umaru Aliyu