An amince da tsagaita wuta a Libiya
August 21, 2020Talla
A wannan Juma'ar ce gwamnatin kasar Libiya wadda Majalisar Dinkin Duniya ta amince da ita, ta sanar da tsagaita buda wuta a fadin kasar tare da kiran janye sojoji musamman a birnin Sirte, yankin da mayakan tawaye suka mamaye.
A wata sanarwa ta daban, bangaren majalisar dokokin Libiya mai hamayya da jagorancin gwamnati ma ya yi kiran a tsagaita buda wutar.
Dukkanin bangarorin biyu na bayyana hakan ne a lokacin da fargaba ke karuwa kan yiwuwar rincabewar al'amura a rikicin na Libiya da aka kwashe shekaru tara ana gwabzawa.
Fayyez al-Sarraj da ke jagorantar gwamnatin ta Libiya, ya sanar da cewar za a yi zaben shugaban kasa da na 'yan majlisa a Libiyar cikin watan Maris na badi.