Amincewa da masu shiga takara a Burkina
October 8, 2020Talla
Daga cikin 'yan takarar da hukumar ta sahalewa tsayawa, har da shugaban kasar mai ci yanzu da ke neman zarcewa akan wa'adin mulki Roch Marc Christian Kaboré da madugun 'yan adawar kasar Zephirin Diabré hakan da wani dadden na hannun damar hambarararen shugaban kasar Blaise Compaoré wato Eddie Komboïgoda kuma firaministan gwamnatin wucin gadi ta mulkin soja da yanzu hakan ke hijira a Canada Yacouba Isaac Zida.
Sai dai hukumar zaben kasar ta ce duk da amincewar da ta yi da 'yan takarar babbar kotun tsarin mulkin kasar ce ke da cikakken hurumi na tantancewa, kana kuma tana da wa'adin kwanaki 10 nan da gaba domin aiwatar da nata bincike. A ranar 22 ga watan Nuwamban wannans hekarar ne za a gudanar da zaben shugaban kasar.