1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An ayyana 'yan Houthi a matsayin 'yan ta'adda

Binta Aliyu Zurmi
January 11, 2021

Sakataren harkokin wajen Amirka Mike Pompeo ya ce Amirka za ta saka mayakan Houthi na kasar Yemen a jerin 'yan ta'adda kasashen ketare.

US-Außenminister Pompeo in Israel
Hoto: Patrick Semansky/Pool/picture alliance

Daga ranar 19 ga watan Janairu ne mayakan za su shiga wannan jerin da ya ayyanasu, kwana guda ke nan kafin sabon shugaba Joe Biden ya kama ragamar mulki.

Haka zalika ana sa ran Mr Pompeo za sake maida kasar Cuba a matsayin kasar da ke taimakawa 'yan ta'adda, batun da ake ganin wani yunkuri ne na dagula wa shugaba mai jiran gado lissafi ta fuskar huldar diflomasiyya tun ma kafin ya hau karagar mulki.