Kotu ta ba da izinin bude masallatai a Jamus
April 30, 2020Wata kungiyar addinnin Islama ce ta arewacin kasar ta kalubalanci matakin gwamnatin kasar ta Jamus na hana gudanar da sallar Juma'a a wannan lokaci na azumin Ramadana a wani masallaci na Jihar Lower Saxony.
A wani zama da ta gudanar a jiya Laraba, kotun kolin kasar ta Jamus ta dauki matakin soke hukuncin da wata kotun da'a a jihar ta yanke a baya na hana gudanar da taruka har a wuraren ibada na Musulmi da Kiristoci da na Yahudawa da nufin hana yaduwar annobar Coronavirus.
A lokacin gabatar da hukuncin dai kotun kolin ta ce matakin da aka dauka a baya ya keta haddin 'yancin gudanar da ayyukan ibada wanda kundin tsarin mulkin kasar ta Jamus ya tanada. A kan haka ne kotun ta ba da izinin ci gaba da taruwa a wuraren ibada duk da cewa cutar na ci gaba da yaduwa a kasar. Sai dai kotun ta gitta sharadin daukar matakan kariya a wuraren ibadar.